(ABNA24.com) Kasashen Afrika sun bukaci hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya da ta gudanar da zaman tattaunawa kan matsalar kabilanci da kuma cin zarafin da ‘yan sanda suke yi.
Gidan rediyon faransa ya bayar da rahoton cewa, jakadan kasar Burkina Faso a Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya wakilci dukkanin kasashen Afrika 54, ya bukaci hukumar kare hakkin bil adama ta majalisar dinkin duniya ta gaggauta gudanar da mahawara kan batun da ya shafi nau’oin nuna wariya da kalibanci, da mummunar dabi’ar nuna rashin tausayi da ‘yan sanda ke yi kan masu zanga-zangar lumana.
Wannan na zuwa ne bayan barkewar zanga-zanga a cikin kasar Amurka sakamakon kisan da ‘yan sanda farar fata suka yi wa George Floyd bakar fata a ‘yan kwanakin da suka gabata, lamarin da ya tayar da hankulan jama’a da dama a duniya.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump yak are ‘yan sanda da suka aikata hakan da cewa, yana da kyau wasu lokuta ‘yan sanda su rika makure wuyan wanda ake zargi da aikata wani laifi.
/129
14 Yuni 2020 - 09:15
Lambar labari: 1046314
Kasashen Afrika sun bukaci hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya da ta gudanar da zaman tattaunawa kan matsalar kabilanci da kuma cin zarafin da ‘yan sanda suke yi.